TAKAITACCEN BAYANI AKAN ALBUM NA BASASA By Alan Waka

TAKAITACCEN BAYANI AKAN ALBUM NA BASASA By Alan Waka

Gajertaccen bayani Akan ko wacce waka da ke wannan Albom na “BASASA” ADDU’O’I ; Waka ce da aka yi ta don sallamawa Allah da mika wiya gareshi, akan shi ke da iko kan dukkan Dangogi na Kaddara mai kyau da kishiyarta. Muna kuma tuba izuwa gareshi bisa ga jarabtar mu da yayi da Masifu wadanda ba za mu iya jurewa ba, babu kuma mai iya yaye mana sai shi kadai. Kuma bama tarayya da kowa acikin Bautarsa.

Na lissafo jahohin Arewa kaf! Sai dai ajizanci in an sami Mantuwa. Na wakilcesu da Addu’a ta neman sauki ga Allah ta’Ala.

RAKA’O’I ; Waka ce da aka yi anfani da salon Labarin sakok kai da kai, akan Rikicin da ke faruwa na cikin Gida ta irin yarda ya ke ritsawa da wanda bai ji ba bai gani ba, kamar dai yarda ta faru da ni a wannan wakar. Shi ne ma Hoton da aka yi amfani da shi a Jikin Bangon ALBUM din. Rikicin da ke haddasa Masifu marasa Misaltuwa.

BASASA ; Waka ce da talke bada labarin matsalar da Rikicin cikin Gida ke Haifarwa kasa ko Jiha, yana karya Tattalin Arzikin kasa ko jiha, yana janyo Musibu da talauci mai kanta, yana gurbata tarbiyya wajen kekasar da zukatan matasa da Bijirewa.

KABILANCI ; Wannan kuma tana kalubalantar Rikicin kabilanci ko Addini ko yare da makamantansu. Allah ya Halicci Mutanen NIG. Ya kaddara haduwarsu Guri guda ga su kuma Mabanbanta yare. A jihar Adamawa kadai mauna da yare kimanin Tamanin da Hudu in an dauke ko wacce jiha. To mu a fahimtarmu menene hikimar Allah da ya kaddara kasantuwarmu a haka? Mun sani Allah ba ya zalunci, kuma ya hana aikata shi ga kowa. Haka ya so ya ganmu kuma tattare da hakan akwai Hikimomi zokar. Me yasa Allah bai yi mu kamar wasu kasashe da ke da yare daya jal! Ba ko kuma ya yi mu duk iri daya don kada a sami banbanci? To rahama ce mu sassaba da junanmu tun daga Harshe Har suna da kamanni. Bibiyi wannan Album a Hankali zaka ji ka kuma karu da fa’idodi a saukake cikin Nisahdi da Halali ba Hluli ba.

JARIDA ; Waka ce da na yi jan hankali akan ‘yan jaridar Ninanci wadanda Allah ya Hore musu Alkalami don waraka da Haske ga Al’uma amma kuma su sai suke amfani da shi wajen muzanci da cinzarafin Al’uma da neman Rashawa da son zuciya. ‘Yan jarida su ne kadai kebabbun mutane da suke fadakarwa akan kowa da komai amm su fadakarwa ta fadi akansu. Shi ne nima na yi tuna sarwa ko nusarwa ko kuma ince tajdidi akan su. Sai na ji gyara in an samu sai in gyara saboda ajizanci. Wadan nan sune wakokin da suka kunshi wannan Mazubi wato BASASA ALBUM.
BONUS

Wannan karon TASKAR ALA sun sake bugo wakokin baya wadanda suka Hada da;

MAKOMA
KAWALWAINIYA ANGARA FUJU’A
FULFULDE
MULUKIYYA
DUNIYA
MAKARANTA
GWADABE
ZAZZAU
SARAKI.

Ku hanzrta mallakar naku ! !

Advertisements
Aside | Posted on by | Tagged | 2 Comments

TA YA YA ZAN LALLASHI ZUCIYA TA GAME DA RABUWAR FUJU’A

DA GASKE NE WAI CIWON SO BAYA WARKEWA ? ? ?

” A farkon lamari da SO ne,
A karshensa ya barkice da ‘ki ne,
Ka so mai sonka saisasa gane,
Watan wataran adawa dawa za ku gane ”

-Alan Waka (KALMAR SO)

Don Allah da gaskene So baya canjawa, ko karewa, haka ma
kuma ciwon so baya warkewa ?

To ni dai ga abin da na fahimta bisa doran ‘yar kuntuwar
fahimtata:

Da farko dai yana matu’kar mahimmanci ka gane cewa So yana
kaiwa can kololuwar sama, haka zalika yana rikitowa zuwa
kasa wanwar, yana zama saisaisa, yana canjawa tare da
juyawa, haka nan dai yana karewa koda kuwa irin son nan da
yake tsakanin Laila da Majnun ko Juliet da Remeo ne, damin
kuwa mun san cewa komai dai farare ne haka nan kuma dai
‘karare ne, ban da Allah Subhanu Wata’ala.

Ciwon So Baya Warkewa ? To ni dai a sanina duk cutar da
Allah ya saukar sai da ya saukar da maganinta. Don ka ga
wance ko wane ba su warkare daga wata cuta ba, ko kuma ma
wata’kila ita ce ta kwantar da su har ta yi ajalinsu,
wannan ba shi yake nuni cewa ba a warkewa daga wannan cutar
ba. Duk wanda ka gani bai warke ba daga wani ciwo ba , to
watakila be yi amfani da sahihin maganin da yakamata ya yi
aiki da shi ba ne.

IDON SO CUTA NE TO HARIMA MAGANI NE, Idon ma har mutum ya
kasa hakurin to akwai wani magainma a wajen Masana halayyar
dan’adam, domin kuwa na ga wani bayani na masana halayyar
dan’adam da yake bayyana cewa idon har ka ga mutum bai
warke daga CIWON SO kada kara ba daya biyu yana matu’kar
yaudarar kansa ne da cewa babu wasu sauran masoya a wannan
rayuwa, ko kuma ma ya d’auka ba zai ta’ba samun madadinsa
ba, kamar yadda ake nunawa a Media (films, novels etc )
kodayaushe, daman a cikin wadancan fina-finan ne a ke nuna
cewa ciwon so baya warkewa, k(uma su d’in ne dai suke yiwa
duk wanda yake cewa so baya karewa ‘tasiri a zuciya ). Duk
wannan kuskuren fahimta ce da wadannan fina-finan suka
haifar a doran kasa. Kai ana ma cikakken yakini tare da
fatan samun ma wanda ya fi shi wancan masoyin da ka ke
tunanin daga shi babu sauran samun farin ciki a gare ka a
cikin wannan rayuwar. Za ka amince da wannan bayanin ne
kawai ta hanyar yin la’akari da lokacin da Allah MaiGirma
ya tashi yin halittarsa sai ya yi su bibbiyu (mace da
namiji) koma fiye da biyun, kamar ka ga akwai: sama da
kasa; wuta da Aljanna; duniya da lahira; wani abin mamaki
da ya tashi yin sama da kasan ba guda dai-dai yai ba tal,
a’a hawa-hawa aka yi su, wuta da aljanna haka suke, haka ma
‘so na gaskiya’ ba guda daya ne ba, haka ma abin yake ga
‘masoyi na gaskiya’ ba guda d’aya ne ba, idon ka rasa
wancan to fa akwai wanda, ya fi sa da Allah zai hada ka
shi, wannan a ganina rahama ce daga Allah Subhanu wata’ala.
Idon ka ga mutum bai warke ba, ko dai bai yi amfani da
sahihin magani ba ne, ko kuma idon ya tashi yin addu’a ba
ya yinta bisa tsarin yadda take, ko kuma idon ya yin, ya
dinga jin cewa ba zai warke ba, adalilin wanke kwakwalwarsa
(brainwashed) da wadancan fina-finan suka yi. Wannan yana
daya daga cikin abin da zan ya’ka a irin wannan kafa ta
watsa bayanai (Media) nan idon har Allah ya sa ina daya
daga cikin Producers ,Mawallafa, ko kuma Mawa’ka !

So Ba Ya Karewa ? Anya kuwa akwai abin da baya ‘karewa kuwa
banda Allah subhanu Wata’ala ?

Game da wannan batu da ake cewa SO baya ‘karewa, akwai
Hadisin nake la’akari da shi kuma shi ne yake yi min tasiri
har Allah ya yi min cikawa, Wato Hadisin na cikin littafin
Mukhutarilhadith wanda Imamu Tirmithy raiwato, da yake
bayyana cewa, ‘Idon zaka so mutum to ka so shi Saisa-saisa,
don watan wata rana zai iya zamowa makiyinka, Haka ma idon
za ka ‘ki ma’kiyinka, ka ‘ki sa saisa-saisa domin kuwa wata
rana zai iya zamowa makiyinka’.

(Kai sai nake ganin kamar wadancan Fina-finan ‘bolywood &
Holywood’ kamar suna sukar wannan Hadisin ne, don kuwa
mafiyansu akwai manufa ta karkashin kasa ake son a cimmawa,
amma ba wai ilimi,nishi ko fadakarwa kawai ba.)

Saboda haka muke cewa, so yana ‘karewa, domin babu ta yarda
da za ayi abubuwa biyu kuma kishiyoyin juna su zamna
zucciya, idon akwai so ‘ki ya zo daga baya dole ne SO kau
daga wajen. ka taba ji wanda yace wallahi ina matukar kin
ka da SON ka ?

Don Allah idon da kyara a min d’ori DANGIN JUNA, mai girman kai ne kawai baya karbar gaskiya.

Wassalam !

Tijjani Abdullahi Musa
(TAMAS MEDIA)

Posted in Uncategorized | Tagged | Leave a comment

SO YANA CANZAWA, SO YANA KAREWA ! !

“So yana karewa, ciwon so yana warkewa, rabuwar masoya yana cire so ko da kuwa son na gaskiya ne”.

Amma kuma wani na ji ya ce wai :

“So! Wani abu ne da baya tsufa, baya k’arewa. Ciwo ne a cikin zuciya wanda baya taba warkewa”

To ku kuma me ku ka ce ?

TO NI DAI GA KADAN DAGA CIKIN DALILAI NA

Da faro dai, mata nawa ne suke da-na-sanin auren mijin aurensu wanda a da take matukar sonsa ???

Me ya ake samun mijin da yake watsawa masoyiyarsa fetur, ko kuma ita ta kone mijin nata ‘kurmus ???

Haka nan kuma Tarin fuka yana chafke SO idon kuma idon kuma ka ce a’a, to ta ya ya za ayi masoyi ya tsallake matarsa ya gudu ya barta yayanta ko su mutu ko kuma su yi rai ? ? ?

So yana kamuwa da masassarar tsintsaye idon kuma ance ba haka ba ne mai yasa ake samun mosoyiyar da take kone masoyinta da ruwan batir ???

So yana kamuwa da ciwon yunwa ko rowa idon kuma ba haka batun yake ba mai ya sa masoyi yake makelewa awajen mai-shayi da biredi, adafe masa wainar kwai ko indomie, ya bar daya rabin ran tasa a gida tana ta gabzar tuwo da miyar kuka ???

Kai so yana kamuwa da cutar shan’inna, kanjamau, mashako, sankarau, cutar tibi kwalara, dds.

A bisa dabi’a ko halayya kamar yadda kowa ya sani ne samari da yammata (masoya) kafinsu yi aure za ka same su suna ta gudanar zazzafar soyayya, kamar a hadiye juna, don tsabar so da soyayya! !

Amma kuma wani abun mamaki, idan ka leka gidajen nasu, bayan wani dan lokaci da aurancewa sai ka sami dadama daga cikin matan suna ta daka uban YAJI kai kace a ramin kunama suke ba a gidan sahibin ba.

To yanzu anan, son karewa ya yi ko kuma ma KARFI ya kara ???

Daga dai cikin wadannan masoyan ake samun masu cewa: ” wallahi zaman ‘ya’yana nake yi da shi amma…” ko
” albarkacin ‘ya’yan take ci, amma…” a nan to ina SON yanan yadda yake ???

Sannan kuma me ya sa ake yawan samun sake-sake aure aka tsakanin masoya, kuma ina son yake da a cewa ba ya canzawa ???

Me ya sa ake samun zagi, cin mutunci, cin amana, cin zarafi, cin fuska ddr. a tsakanin masoya Musamman ga ma’aurata ???

Me ya sa mace za ta auri namiji su yi shekara 15 tare, suna ta soyayya, amma ranar da Azara’ilu ya zo ya dauke mijin, sai ‘yan koke-koke da ‘yan murje-murje, bayan ‘yan watanni sai ka ji ta sake wani auren? Shin wannan shi ne so da soyayyar a da cewa ba ya karewa ba? Me zai hana ta zauna ba aure har abada tun da shi ruhin rayuwar nata ya tafi ???

So yana canzawa kamar yadda zuciyar masoyan take chanjawa ! !

Ciwon so yana warkewa kamar yadda masoyan suke warkewa daga rashin lafiya mai matukar tsanani.

So yana karewa kamar yadda masoyan suke karewa su bar duniya dungurungum, ko da kuwa son saboda Allah ake yinsa ! !

Aside | Posted on by | Leave a comment

HOW TO MAKE A MARK IN THIS BIASED AND VAIN WORLD,

FOLLOW THESE RULE

-Believe while others are
doubting.

-Plan while others are playing.

-Study while others are
sleeping.

-Decide while others are
delaying.

-Prepare while others are daydreaming.

-Begin while others are
procastinating.

-Work while others are
wishing.

-Save while others are wasting.

-Listen while others are
talking.

-Smile while others are
frowning.

-Commend while others are criticizing.

-Persist while others are
quitting.

And you’ll always be
the best of the best in
wherever
you find yourself.

Posted in Living, Motivation | Tagged | Leave a comment